Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shugaban hukumar zaben kasar Libya Imad al-Sayeh, ya fada a jiya Lahadi cewa, hukumar za ta bude kofar rajistar ‘yan takara a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a watan Nuwamba.
Al-Sayeh ya kara da cewa za a fara aikin rajistar ne a tsakiyar watan Nuwamba idan aka kammala shirye-shiryen da suka kamata da kuma kammala kayan aiki.
Zaben dai babban mataki ne a kokarin kawo karshen tashe-tashen hankulan da aka kwashe shekaru goma ana yi ta hanyar kafa sabon shugabanci na siyasa tare da halattacciyar doka a kasar ta Libya.
A ranar Alhamis ne firaministan kasar Libya Abdel Hamid al-Dabaiba da wasu kasashen ketare suka amince da gudanar da babban zaben kasar a ranar 24 ga watan Disamba.
Haka nan kuma an bayyana a wani shirin zaman lafiya da MDD ke marawa baya da nufin kawo karshen tarzoma da rarrabuwar kawuna da suka addabi kasar tsawon shekaru.
342/